Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Ra'ayoyin Masu Sauraro kan janye yajin aikin Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya
15/09/2025 Duración: 09minShirin Ra'ayoyin Mai Sauraro na wannan Litinin tare da Nasiru Sani ya tattauna ne kan janye yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar da ƙugiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta sanar a ƙarshen mako, kwanaki bayan fara ta a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta ƙara wa'aɗin makwanni biyu don a biya musu buƙatunsu. Daga cikin buƙatun ƙungiyar da take nema gwamnati ta biya akwai abinda ya shafi albashi da alawus-alawus da kuma walwalar mambobinta. Ku latsa alamar sauti domin sauraron ra'ayoyin wasu daga cikin masu sauraro da suka aikoma ta manhajarmu ta Whatsapp
-
Ra'ayoyin masu saurare kan matakin Najeriya na haramta zirga-zirgar jiragen ruwa marasa lasisi
11/09/2025 Duración: 09minA yunƙurin rage yawaitar haɗura akan ruwa, Hukumar Kula da Zirga-zirga a kan Kogunan Najeriya ta haramta yin amfani da jiragen ruwa a kan kogunan ƙasar sai tare da samun izini daga gare ta. Wasu daga cikin matakan da hukumar ta sanar sun haɗa da hana yin lodin fasinja sai a tashoshin da ta amince da su, sai tilasta wa fasinja yin amfani da rigar kariya, da mallakar takardar shaidar ƙwarewa ga illahirin matuƙan jiragen da dai sauransu. Anya waɗannan matakai za su taimaka don rage afkuwar haɗurra a kan kogunan Najeriya? Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ƴancin faɗar albarkacin baki a Nijar
10/09/2025 Duración: 08minA Jamhuriyar Nijar, batun ƴancin faɗin albarkacin baki, aikin jarida ko kafa ƙungiyoyi da sunan yi fafutuka na ci gaba da fuskantar barazana. Bayan rusa ilahirin jam’iyyun siyasa, daga bisani an ci gaba da kama ƴan jarida da masu fafutukar kare hakkin bil adama, tare da jefa ƙungiyoyin kwadago a cikin fargaba ta hanyar farawa da rusa kungiyoyin alƙalai na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don jin ra'ayoyin jama'a kan wannan batu.
-
Ra'ayoyin masu sauraren kan rikicin NUPENG da Dangote a Najeriya
08/09/2025 Duración: 10minA Najeriya, an shiga takun-saƙa tsakanin Ƙungiyar NUPENG ta direbobin motocin dakon mai da iskar gas da kuma Ɗangote wanda ya sanar da sayo motoci dubu 4 da zai yi amfani da su don rarraba man fetur a sassan ƙasar. Yayin da NUPENG ke cewa magoya bayanta ne ke da hurumin raba mai da iskar gas a ƙasar, sai dai manazarta na cewa Ɗangote, na da damar raba hajarsa sakamakon sakin mara da aka yi wa ɓangaren kasuwanci a ƙarƙashin dokokin Najeriya. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi....
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa daban-daban
05/09/2025 Duración: 10minKamar yadda aka saba kowacce ranar Juma'a mukan baku dama don bayyana mana ra'ayoyinku game da batutuwa daban-daban da suka shafin fannonin rayuwa daban-daban don kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo ɗauki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu Garba
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kama Simon Ekpa mai fafutukar kafa ƙasar Biafra
03/09/2025 Duración: 10minKotun ƙasar Finland ta ɗaure Simon Ekpa mai fafutukar kafa ballewar Biafra daga Najeriya shekaru 6 a gidan yari, saboda samun sa da laifufukan ta’addanci. Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin ake ci gaba da tsare ɗaruruwan mutane a gidajen yarin Najeriya bisa zargin aikata ta’addanci, amma kotuna sun gaza hukuntar da su. Shin ko me za ku ce a game da wannan hukunci da kotun ƙasar Finland ta yanke? Meye ra’ayoyinku a game da gazawar kotunan Najeriya wajen hukunta waɗanda ake tuhuma da aikata irin waɗannan laifuka a cikin gida? Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu
-
Ra'ayoyin masu saurare kan taron manyan hafsoshin tsaron Afrika
27/08/2025 Duración: 09minHafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka a taron da suka yi a birinin Abujan Najeriya, sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta. Wannan taro dai ya samu halartar wakilan ƙasashe sama da 50, waɗanda suka yi imani da cewa la’akari da girman matsalar, akwai buƙatar ƙasashen su yi aiki a tare don tunkarar ta. Shin ko meye ra’ayoyinku a game da wannan yunƙuri na ƙasashen Afirka? Waɗannan shawarwari za ku bayar domin samun nasarar wannan fata? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
-
Ra'ayoyin masu sauraren kan yadda ɗimbin mutane suka rasa ayyukansu a Nijar
25/08/2025 Duración: 11minA jamhuriyar Nijar, dubban mutane ne suka rasa ayyukansu yayin da ɗimbin ƴan gudun hijira suka daina samun tallafi, bayan da mahukunta suka kori mafi yawan ƙungiyoyin agaji daga gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar. Bayan korar waɗannan ƙungiyoyi da ke taimaka wa ƴan gudun hijira, a mafi yawan yankuna har yanzu gwamnatin ta gaza samar da tsarin da zai maye gurbin waɗannan ƙungiyoyi don agaza wa jama’a. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa da dama
22/08/2025 Duración: 06minYau Juma'a rana ce da mukan baiwa masu saurarenmu damar tofa albarkacin bakinsu a cikin shirinmu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikaken shirin tare da Nasiru Sani
-
Ra'ayoyin masu saurare kan alfanun sulhu da 'yanbindiga ko akasanin haka a Najeriya
21/08/2025 Duración: 10minA Najeriya muhawara ta ɓarke game da buƙatar sulhu da ƴan ta’adda maimakon amfani da ƙarfin Soji, kodayake an samu mabanbantan ra’ayoyi daga ɓangaren masana a fannin na tsaro lura da yadda suka ce irin wannan sulhu ya gaza amfanarwa a yankuna da dama duk da cewa anga alfanunsa a wasu yankunan. Yaya kuke kallon wannan batu? Shin kuna ganin sulhu ko kuwa amfani da ƙarfin soji shi ne mafi a’ala wajen yaƙi matsalolin tsaron Najeriyar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkaci bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza....
-
Ra'ayoyin masu saurare kan shirin rungumar GMO a Najeriya
19/08/2025 Duración: 10minLura da yadda jama’a ke ɗari-ɗari a game da kayan abincin da aka sauya wa ƙwayoyin halitta da ake kira GMO, wannan ya sa mahukunta a Najeriya ke neman yin amfani da malaman addini domin gamsar da jama’a su rungumi irin wannan abinci. Abin neman sani a nan shi ne, shin ko kun fahinci abin da ake kira GMO? Ko a shirye ku ke domin karɓar nau’in abincin da aka canza wa ƙwayoyin halitta? Anya yin amfani da malaman addini zai sa jama’a su amince da shi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kama jagororin ƙungiyar Ansaru a Najeriya
18/08/2025 Duración: 10minMai Bai wa Shugaban Najeriya Shawara kan Sha’anin Tsaro Nura Ribaɗo ya tabbatar da kama jagororin ƙungiyar Ansaru da ake kira Ƴan Mahmuda su biyu, waɗanda suka jima suna addabar yankunan ƙasar. Ana dai bayyana wannan ƙungiya a matsayin babbar barazana ga matsalar tsaron ƙasar, saboda alaƙarta kai-tsaye da Alqa’ida. Shin ko wane sauyi wannan kame zai samar ta fannin tsaro a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
15/08/2025 Duración: 09minYau take ranar bayyana ra'ayoyinku kan batutuwa da suke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, zamantewa da sauran abubuwan daban daban na rayuwa. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan yajin aikin lauyoyi a Nijar
14/08/2025 Duración: 09minLauyoyi a Jamhuriyar Nijar sun tsunduma yajin aikin kwanaki biyu daga yau Alhamis, domin nuna rashin amincewa da rusa ƙungiyoyin alƙalai da sauran ma’aikatan shari’a da gwamnatin ƙasar ta yi. Kafin rusa waɗannan ƙungiyoyi, tuni aka rusa ƙungiyoyin jami’an kare gandun daji da na kwastam da kuma illahirin jam’iyyun siyasar ƙasar. Shin, ko me za ku ce a game da wannan mataki na gwamnatin Nijar ta ɗauka? A irin wannan yanayi, ko meye makomar ƴancin gudanar da ƙungiyoyi a ƙasar? Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi...
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda Bankin Duniya ya rantawa Najeriya dala miliyan 300
13/08/2025 Duración: 10minBankin Duniya ya amince ya ranta wa Najeriya dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 460 don tallafa wa mutanen da suka ƙaurace wa matsugunansu saboda matsaloli a sassa daban daban na Arewacin ƙasar. Yanzu haka akwai mutane sama da milyan 3 da rabi da ke rayuwa a wannan yanayi, kuma mafi yawansu sun dogara da tallafi ne domin rayuwa. Shin ko waɗanne matakai suka kamata a ɗauka don tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen ta hanyoyin da suka dace? Sai ku bayyana ra’ayoyinku a lambarmu ta Whatsapp da kuma shafinmu na Facebook.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan yadda ake samun ambaliyar ruwa a irin wannan lokaci
12/08/2025 Duración: 10minKusan a kowacce shekara, dai-dai wannan lokaci ne ake samun faruwar ambaliya sakamakon saukar ruwan sama mai yawa da ke haddasa asarar rayuka da kuma dukiyoyi masu tarin yawa. A daidai wannan lokaci, ko wane hali ake ciki a yankunanku dangane da batun ambaliya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a wannan rana. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan matakin Nijar na ƙwace kamfanonin haƙar zinare
11/08/2025 Duración: 10minGwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace ilahirin kamfanonin haƙo zinare tare da shelanta cewa sun zama mallakin ƙasar, yayin da a ɗaya ɓangare ta hana fitar da duk wani nau’in dutse mai ƙima zuwa ƙetare sai tare da izinin hukuma. Hakan na zuwa ne watanni bayan ta ƙwace kamfanonin haƙo uranium matsayin mallakin ƙasar. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Waɗanne abubuwa ne suka fi ci muku tuwa a ƙwarya
08/08/2025 Duración: 10minShirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana kamar yadda aka saba ya baku damar fadɗn albakacin bakinku kan abubuwan da suka fi ci muku tuwo a ƙwarya a fannin lafiya, jagoranci, siyasa da kuma zamantakewa. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kalaman Falana game da matakan tattalin arziƙin Tinubu
07/08/2025 Duración: 10minBisa ga al’ada, ana cewa al’umma ta kasu ne zuwa rukuni uku, wato attajirai, da matsakaita sai kuma matalauta. To sai dai a cewar shahrarren lauya kuma mai fafutuka Femi Falana, a Najeriya mutane na rayuwa ne a ɗaya daga cikin rukuni biyu kawai: wato gungun attajirai ko kuma na talakawa, wannan kuwa sakamakon ɓullo da sabuwar siyasar tattalin arziki maras alfanu a ƙasar.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan zanga-zangar neman korar 'yan Najeriya daga Ghana
31/07/2025 Duración: 09minA ƴan kwanakin nan an samu ɓarkewar zanga-zangar a Ghana, inda ƴan ƙasar ke zargin ƴan Najeriya da ke can da aikata laifuka kisan gilla da karuwanci, lamarin da ya sa masu zanga-zangar neman a koresu daga ƙasarsu. Haka nan masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa ƴan kasuwan Najeriya sun mamaye musu kasuwanni tare da karya dokokin kasuwanci a ƙasar. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...