Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan sabon matakin zaftare kuɗaɗe don ceto ƙasa a Nijar
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:10:28
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Ra’ayoyi sun sha bambam a tsakanin al’umma dangane da matakin zaftare kuɗaɗe don tallafa wa Gidauniyar Ceton Ƙasa da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kafa. Ƙarƙashin wannan gidauniya, kusan kowane rukuni na jama’a, tun daga ƙusoshin gwamnati, zuwa ma’aikata da kamfanoni, na gwamnati da masu zaman kansu, kai har ma da masu zaman kashe wando, ala dole sai kowa ya bayar da nasa tallafin. Shin me za ku ce a game da wannan Gidauniya, da har ake cewa har yanzu ba wanda ke da hurumin gudanar da bincike dangane da kuɗaɗen da ake tarawa a cikinta? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...