Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu saurare kan yawaitar yajin aikin likitoci a Najeriya

Informações:

Sinopsis

Yawaitar yajin aikin likitoci na neman kassara ɓangaren kiwon lafiya a Najeriya, domin kuwa yanzu haka likitocin da suka kammala karatu sannan suke cikin asibitoci don sanin makamar aiki, sun tsunduma yajin aiki saboda neman a biya su haƙƙoƙinsu kamar dai yadda yake ƙunshe a yarjejeniyar da ke tsakaninsu da hukuma. Shin ko yaya wannan yajin aiki ke shafar sha’anin kiwon lafiya a yankunan da ku ke rayuwa? Wace shawara za ku bai wa ɓangarorin don warware saɓanin da ke tsakaninsu? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...