Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu saurare kan tasa ƙeyar 'yan damfara da Najeriya ta yi zuwa ƙasashensu

Informações:

Sinopsis

Mahukunta a Najeriya sun tasa ƙeyar ƴan asalin ƙasashen waje su 192 da aka tabbatar da sun shahara wajen aikata damfara ta yanar gizo a cikin ƙasar. Mutanen waɗanda aka kama a birnin Lagos, sun haɗa da China, Philippines, Malaysia, Pakistan, Tunisia da dai sauransu, waɗanda tuni kotu ta tabbatar da laifukansu. Shin me za ku ce a game da yadda ƴan damfara a yanar gizo ke neman mayar da Najeriya a matsayin tunga domin baje kolinsu? Shin ko kun gamsu da irin matakan da mahukunta ke ɗauka domin daƙile wannan matsala?  Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...