Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Ra'ayoyin masu saurare game da yadda ICPC ke sanya ido kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi
17/09/2025 Duración: 10minHukukumar Yaƙi da Rasha ta ICPC a Najeriya, ta ce yanzu haka tana ƙara sa-ido dangane da yadda ake kashe kuɗaɗe mallakin ƙananan hukumomi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ke shan matsin lamba domin ganin ta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya buƙaci a zuba wa ƙananan hukumomin kuɗadensu kai-tsaye a maimakon bi ta hannun gwamnonin jihohi. Ko me za ku ce a game da jan ƙafa wajen aiwatar da wannan umarni da kotu ta bayar tun watan Yulin shekara ta 2024 da ta gabata? Wace irin rawa ya dace ICPC ta taka don kare dukiyar ƙananan hukumomi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakin ku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Ra'ayoyin Masu Sauraro kan janye yajin aikin Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya
15/09/2025 Duración: 09minShirin Ra'ayoyin Mai Sauraro na wannan Litinin tare da Nasiru Sani ya tattauna ne kan janye yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar da ƙugiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta sanar a ƙarshen mako, kwanaki bayan fara ta a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta ƙara wa'aɗin makwanni biyu don a biya musu buƙatunsu. Daga cikin buƙatun ƙungiyar da take nema gwamnati ta biya akwai abinda ya shafi albashi da alawus-alawus da kuma walwalar mambobinta. Ku latsa alamar sauti domin sauraron ra'ayoyin wasu daga cikin masu sauraro da suka aikoma ta manhajarmu ta Whatsapp
-
Ra'ayoyin masu saurare kan matakin Najeriya na haramta zirga-zirgar jiragen ruwa marasa lasisi
11/09/2025 Duración: 09minA yunƙurin rage yawaitar haɗura akan ruwa, Hukumar Kula da Zirga-zirga a kan Kogunan Najeriya ta haramta yin amfani da jiragen ruwa a kan kogunan ƙasar sai tare da samun izini daga gare ta. Wasu daga cikin matakan da hukumar ta sanar sun haɗa da hana yin lodin fasinja sai a tashoshin da ta amince da su, sai tilasta wa fasinja yin amfani da rigar kariya, da mallakar takardar shaidar ƙwarewa ga illahirin matuƙan jiragen da dai sauransu. Anya waɗannan matakai za su taimaka don rage afkuwar haɗurra a kan kogunan Najeriya? Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ƴancin faɗar albarkacin baki a Nijar
10/09/2025 Duración: 08minA Jamhuriyar Nijar, batun ƴancin faɗin albarkacin baki, aikin jarida ko kafa ƙungiyoyi da sunan yi fafutuka na ci gaba da fuskantar barazana. Bayan rusa ilahirin jam’iyyun siyasa, daga bisani an ci gaba da kama ƴan jarida da masu fafutukar kare hakkin bil adama, tare da jefa ƙungiyoyin kwadago a cikin fargaba ta hanyar farawa da rusa kungiyoyin alƙalai na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don jin ra'ayoyin jama'a kan wannan batu.