Bakonmu A Yau

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 1:32:01
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Ambasada Yusuf Tuggar kan ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS

    29/01/2025 Duración: 03min

    Tattaunawar ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar da Mohammed Sani Abubakar  kan batun cikar wa'adin ƙasashen ficewar ƙasashen AES na Mali, Burkina Faso da Nijar daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS. Latsa alamar sauti domin sauraren yadda tattaunawar ta kasance...

  • Prof Peter Lassa kan zargin majalisun Najeriya da neman cin hanci daga jami'oi

    28/01/2025 Duración: 03min

    Wani bincike ya zargi kwamitin ilimi na majalisun Najeriya ta bukatar naira miliyan takwas takwas daga kowanne shugaban jami'ar tarayya kafin amincewa da kasafin kudinsu na wannan shekarar. Tuni wannan zargi ya haifar da cece kuce a cikin kasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Peter Lassa, tsohon shugaban hukumar gudanarwar manyan kwalejojin ilimin Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana...........

  • Malam Isma’il Ahmad kan buƙatar Trump na kwashe Falasɗinawa daga Gaza

    27/01/2025 Duración: 03min

    Bayan shafe watanni 15 ana gwabza mummunan yaƙi a yankin Gaza tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan Hamas da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, shugabaan Amurka, Donald Trump ya ce yaƙin ya lalata yankin na Gaza baki daya, don haka ya bayyana wa Sarki Abdallah na Jordan  buƙatar kwashe Falasɗinawa daga yankin zuwa ƙasarsa kuma ya ce ya na  sa ran tattaunawa da shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi a kan haka.  A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da masanin lammuran da suka shafi Gabas ta Tsakiya, Malam Isma’il Ahmad.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............

  • Sule Ammani kan gurfanar Obasanjo da Buhari gaban wata kotu a Faransa

    24/01/2025 Duración: 03min

    Tsoffin shugabannin Najeriya guda 2 wato Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari sun gurfana a wata kotun sasanta rikicin kwangilla domin bada ba'asi a kan soke kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ministan Obasanjo ya bayar bada saninsa ba, da kuma kin biyan kudin sasanta matsalar da gwamnatin Buhari ta ki. Dangane da wannan dambarwa Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da daya daga cikin dattawan kasar Alhaji Sule Ammani,  Yarin Katsina.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyartattaunawar.

  • Dr Adamu Tilde kan faɗuwar farashin kayan abinci a Najeriya

    23/01/2025 Duración: 03min

    Rahotanni daga sassan Najeriya sun nuna cewar an samu faduwar farashin kayan abinci bayan jama'ar ƙasar suka kwashe dogon lokaci suna fama da tsadarsa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Adamu Tilde, masanin harkar noma kuma ɗan kasuwa dangane da lamarin. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........

  • Farfesa Balarabe Sani kan manufofin gwamnatin Donald Trump na Amurka

    22/01/2025 Duración: 03min

    Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga cikin mambobin Hukumar Lafiya ta Duniya, matakin da wasu ke ganin na iya illa ga dorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya. Dangane da tasirin matakin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Dr Abdulhakeem Garba Funtua kan sabon wa'adin Donald Trump a Amurka

    21/01/2025 Duración: 03min

    Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana manufofin gwamnatinsa bayan karbar rantsuwar kama aiki da ya yi a matsayin shugaba na 47. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar kwalejin Fasaha ta Kaduna dangane da wadannan manufofi, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.

  • Tattaunawa da Daraktan Amnesty Isa Sanusi kan yawaitar haɗarin tankar mai a Najeriya

    20/01/2025 Duración: 03min

    Ƙungiyar Amnesty International ta danganta haɗrin tankin man da ya hallaka kusan mutane 100 a jihar Neja ta tsakiyar Najeriyar a matsayin talaucin da ya yiwa jama'ar ƙasar katutu,  inda daraktan ƙungiyar a Najeriyar Malam Isa Sanusi ke cewa akwai buƙatar mahukunta su sassauta matakan da suke ɗauka a lamurran da suka shafi tattalin arziƙi. Matsalar ta haɗari ko kuma gobarar tankar mai na neman zama ruwan dare a Najeriya, inda ko a baya-bayan nan aka ga yadda fiye da mutane 100 suka mutu can a jihar Jigawa sakamakon gobarar da ta tashi lokacin da suke tsaka da kalen man da ya malala akan titi bayan tuntsirewar wata tanka.Masana irin daraktan ƙungiyar ta Amnesty International mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Isa Sanusi na kallon talauci a matsayin babban dalilin da ke sanya mutane kai kansu ga irin wannan haɗarin wanda ke nuna buƙatar da ke akwai ga mahukunta wajen sun samar da sassauci ga jama'a don kaucewa fuskantan makamantan wannan matsaloli.Yayin wata zantawarsa da editan sashen Hausa na RFI Bashir Ibrahim I

  • Zantawa da babban Editan Jaridar Aminiya Malam Sagir Kano Saleh

    17/01/2025 Duración: 02min

    Kamar yadda aka saba a kowacce ranar Juma'a, jaridar Aminiya da ake wallafawa a Najeriya ke fita kuma Abida Shuaibu Baraza ta tattauna da Editan Jaridar Malam Sagir Kano Saleh domin jin abin da ta ƙunsa. sai latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar.

  • Dokta Abdulhakim Garba Funtua kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    16/01/2025 Duración: 03min

    Isra'ila da kungiyar Hamas sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen yakin da suka kwashe watanni 15 suna fafatawa, wanda ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa sama da dubu 45, bayan harin da ya kashe Yahudawa sama da dubu guda. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar duniya Dr Abdulhakeem Garba Funtua game da yarjejeniyar, kuma ga yadda zantawasu ta gudana a kai. 

  • Dr. Yahuza Getso kan ta'azzarar matsalolin tsaro a ƙasashen Afirka

    15/01/2025 Duración: 07min

    Matsalolin tsaro na kara ta’azzara a ƙasashen Afirka masamman a Sahel da tafkin Chadi, inda aka ga yadda Boko Haram ke zafafa kai hare-hare a sansanoni da cibiyoyin jami’an tsaro a jihar Barno, yayin da mahara masu ikirarin jihadi suka tsanata kai farmaki a ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Fado, ko a ranar Alhamis ƴan ta’adda sun kashe sojojin Benin kusan 30 a wani hari da suka kai arewacin ƙasar, sai kuma wani hari da ƴan bindiga suka kai fadar shugaban ƙasar Chadi da gwamnati ta  daƙile. A tattaunawarsa da Ahmed Abba, Dr. Yahuza Ahmad Getso masanin tsaro a Najeriya, ya ce duk da yadda ƙasashen ke ikirarin yaƙi da matsalolin tsaro, ba su da cikakkun tsare-tsaren da suka dace a bangaren soji da tafiyar da gwamnati, halisama ba da gaske su ke yi ba.

  • Abdoul Nasir kan matakin gwamnatin Nijar na hukunta baƙi marasa takardu

    15/01/2025 Duración: 03min

    Hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar sun gabatar da wata sabuwar dokar da zata hukunta baƙin da ke shiga cikin kasar ba tare da halartattun takardu ba. Wannan ya biyo bayan zarge zargen da ake na samun wasu baki da ke yiwa kasar zagon kasa. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai sharhi a kan Nijar, Abdoul Naseer, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. 

  • Tijjani Gamawa a kan ƙuraƙuran da sojin saman Najeriya ke yi kan farar hula

    14/01/2025 Duración: 03min

    'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi daban daban dangane da harin saman da sojoji suka kai a kan 'Yan sakai a Jihar Zamfara, wanda ya hallaka akalla mutane 15. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar tsaro kuma tsohon sojin sama Air Commodore Tijjani Baba Gamawa kan lamarin, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.   

  • Janar Pascal Lanni kan ficewar dakarun Faransa daga Chadi

    13/01/2025 Duración: 03min

    A ranar Asabar ce Faransa ta mika sansanin sojinta na biyu a kasar Chadi ga mahukuntan kasar a wani bangare na janye sojojinta a karshen watan Janairu.Kimanin sojoji Faransa 100 ne suka bar sansanin Abéché a ranar Asabar, kafin janye na Djamena su kusan 1000.A tattaunawarsa da Ibrahima Timbi Bah, Editan sashin Fulatanci na RFI, kwamandan dakarun Faransa a Afrika Janar  Pascal Lanni ya yi karin haske kan ficewarsu daga Afirka. 

  • Abdullahi Bakoji kan harin Boko Haram da ya yi ajalin sojoji a najeriya

    08/01/2025 Duración: 03min

    Masana tsaro na ci gaba da tsokaci kan harin da mayakan Boko Haram suka kai sansanin sojin Damboa a jihar Bornon Najeriya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji da ƴan sa kai. Kan hakan ne wakilinmu Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi ya tuntuɓi masanin tsaro Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya.Shiga alamar sauti, domin sauraron ciakkiyar tattaunawar.

  • Dr Yahuza Getso kan gudunmawar ƴan sa kai a yaki da ta'addanci a Najeriya

    06/01/2025 Duración: 03min

    A Najeriya jami’an tsaro na ‘Yan Sa-kai ko Vigilante ko kuma na ‘Civilian JTF’ da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na taka rawa wajen taimakawa jami’an tsaro na gwamnati wajen yaƙi da ta’addanci da sauran miyagun laifuka. Sai dai duk da ƙokarin jami’an tsaron na Sa-Kai ra’ayoyi sun banbanta, dangane da rawar da suke takawa, inda wasu ke yaba musu ɗari bisa ɗari, yayin da wasu ke neman a yi gyara kan tsarin ayyukansu la’akari da kura-kuran sukan tafka ta hanyar wuce gona da iri a wasu lokuta da dama.Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro a tarayyar Najeriya, Dakta Yahuza Getso.

  • Ambasada Abdullahi Bindawa: Gudunmawar marigayi Jimmy Carter ga duniya

    03/01/2025 Duración: 03min

    Ana ci gaba da jimamin mutuwar tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter wanda ke shan jinjina saboda irin gagarumar rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma ingantan rayuwar talakawa a ƙasashen Afrika da suka haɗa da Najeriya da Nijar. Ambasada Abdullahi Bindawa, na ɗaya daga cikin jami’an da suka yi aiki kut da kut tare da Jimmy Carter, ga kuma abin da yake cewa kan marigayi a hirarsa da Abdurrahman Gambo AhmadKu latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu

  • Farfesa Kabir Ɗandago kan ma'aunin tattalin arzikin Najeriya a bara da kuma bana

    03/01/2025 Duración: 09min

    Ƴan Najeriya na fatan ganin samun sauƙi a wannan shekara ta 2025, bayan da suka shiga wani yanayi na matsalin tattalin arziki a shekarar 2024 da muka yi bankwana da ita, sakamkon wasu matakai da gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka, masamman janye tallafin man fetur da kuma barin naira ta ceci kanta a kasuwar canjin kuɗaɗe. Shugaban ƙasar Bola Tinubu dai ya ce gwamnatinsa za ta rage hauhawar farashi a shekarar 2025 ta hanyar haɓaka noma da tallafa wa masana'antu, danage da fatan da ƴan Najeriyar ke da shi da kuma hasashen masana dangane da farfadowa tattalin arziki a wannan shekara, Ahmad Abba ya tattauna da Farfesa Kabiru Isa Dandago na jami’ar Bayaro da ke Kano, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

  • Isah Sunusi kan hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza da ke ci gaba da lakume rayuka

    01/01/2025 Duración: 03min

    Ƙungiyar kare hakkin bil Adama ta ‘Amnesty International’, ta fitar da sakamakon binciken da ta gudanar akan zarge-zargen da ake yi wa Isra’ila na aikata kisan ƙare dangi a Gaza. Cikin rahoton wanda aka fitar da shi a birnin Kano dake arewacin Najeriya, Amnesty tace Isra’ila ta kashe mutane sama da dubu 40, ciki harda kananan yara dubu 13 a cikin shekara guda.Wakilinmu na Kanon Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo ta tattauna da Daraktan kungiyar ta Amnesty a Najeriya Isa Sunusi.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Auwal Musa Rafsanjani kan neman shugaba Tinubu da muƙarrabansa su bayyana kadarorinsu

    30/12/2024 Duración: 03min

    Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta buƙaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da ministoci da gwamnoni da su bayyana wa al’ummar ƙasar kadarorin da suka mallaka, a wani mataki na yaƙi da matsalar wawure dukiyar talakawa. A game da wannan batu, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da shugaban CISLAC da ke yaƙi da rashawa a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.........

página 1 de 2