Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Rundunar tsaron Najeriya ta mayar wa Nijar martani kan zargin yi mata zagon ƙasa
27/12/2024 Duración: 02minRundunar Tsaron Najeriya ta mayar da martani kan kalaman shugaban soji na Nijar, bisa zarge-zargen da ya yi kan ƙasar na cewa tana haɗa kai da Faransa domin yi mata maƙarƙashiya. Latsa alamar sauti domin sauraren ƙarin bayanin da kakakin rundunar tsaron Najeriya Birgediya Janar Tukur Gusau ya yi wa wakilinmu na Abuja Mohd.Sani Abubakar...
-
Barista Ibrahim Cheɗi kan rahoton ICPC na ayyukan rashawa a ma'aikatun gwamnati
26/12/2024 Duración: 03minA ‘yan kwanakin da suka gabata, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya ta fitar da rahoton cewa, kotun ƙolin ƙasar haɗi da wasu hukumomin gwamnati 14, sun gaza cin jarabawar nagarta da ɗa’a da ta ke yi, domin duba ayyukan rashawa a faɗin ƙasar a duk shekara. Hauwa Halliru Gwangwazo ta tattauna da masanin shari’a a ƙasar, Barista Ibrahim Abdullahi Cheɗi, kan yadda su ke kallon girman matsalar a mahangar su ta shari’a.Latsa alamar sauti domin sauraren yadda tataunawarsu ta kasance...
-
Joseph Nahum kan bubuwan ranar Kirismeti a sassan duniya
25/12/2024 Duración: 03minMabiya addinin Kirista na cigaba da bukukuwan zagayowar ranar Kirsimeti a sassan duniya don tunawa da ranar haihuwar Yesu Al Masihu da aka yi a Bethlehem da ke kudu da birnin Qudus. Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin Kirista suka kwashe suna gudanar da wannan biki a duk fadin duniya, ta hanyar nuna farin ciki da ƙauma da tausayin juna da sadaukarwa da dai sauransu.Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Reverend Joseph Nahum, dake garin Maiduguri, wanda ya fara da yin tsokaci kan muhimmancin ranar ta Kirsimeti.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Amb Abubakar Cika kan mataki AES na zaman rundunonin sojinsu cikin shirin ko ta kwana
24/12/2024 Duración: 03minƘasashen AES da suka haɗa da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso sun yi watsi da ƙarin wa’adin watanni shidda da ECOWAS ta yi musu a makon jiya, kan lokacin ficewarsu daga cikin ƙungiyar a hukumance, rangwamen da zai fara aiki a watan Janairun dake tafe. Cikin sanarwar da suka fitar, ƙasashen uku sun sanar da baiwa rundunonin sojinsu umarnin zama cikin shirin kar ta kwana. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Ambassada Abubakar Cika tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu..................