Kasuwanci

Majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan yawaitar harajin Bankuna

Informações:

Sinopsis

A 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan karon, ya mayar da hanhali ne kan binciken da Majalisar Walikan Nigeria ta ƙaddamar dangane da ƙorafin ƴan ƙasar kan maban-banta haraji da Bankuna ke yawaita cirewa a asusun ajiyarsu. A ƙarshen watan oktoban da ya gabata ne, Mjalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin da ta dorawa alhakin bin diddigin korafe-korafen da masu ajiya a bankuna ke yi kan yawan cire musu kudade da ake yi daga asusun ajiyarsu na banki. Kaddamar da kwamitin, ya biyo bayan tarin korafe korafen da ƴan Nigeria ke yi, musamman masu ajiyar kudi a bankunan kasar, game da yawan cire musu kudade ba-gaira ba dalili da bankunan ke yi, da sunan wasu ayyuka da bankunan ke ikirarin gudanarwa. Masana na alakanta wannan batu, da nau’o’in harajin da ake da su a kasar, a matakin kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya, yayinda wasu ma’aikatan gwamnatin kasar, ke kukan cewa wasu kudaden da ake cire musu, musamman na gidaje da na pansho, ba a tura su ga hukumomin da suka dace. Ku latsa alamar sauti don s