Kasuwanci
Tasirin ƙarin harajin kashi 15 da Najeriya ta sanya kan man da ake shigarwa ƙasar
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:10:07
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Shirin a wannan makon ya yi dubi ne akan batun sabon harajin kashi 15 da gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanya kan tataccen man fetur da dangogin sa da ake shigo da su ƙasar daga ketare, ala’marin da ya fara jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar kan yuwuwar tashin farashin litar man na fetur. A ranar Jumma’ar da ta gabata ce, fadar gwamnatin Najeriya, ta sanar da cewa tuni shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da harajin fito na kashi 15 kan man fetir da dizal da za a shigo da su ƙasar daga waje, yana mai bayyana tsarin, a matsayin matakin bunƙasa matatun mai na cikin gida da kuma dogaro da kai a fannin makamashi. Sai dai, tuni dilllalan man fetur a ƙasar suka fara gargaɗin cewar muddin karin ya tabbata to akwai yuwuwar farashin man fetur da dangoginsa ya yi tashin da zai fi ƙarfin da yawa daga cikin al’ummar ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........