Wasanni
An fara gasar Super Ligue ta Jamhuriyar Nijar
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:09:59
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Shirin duniyar wasanni na wannan mako zai maida hankali a kan yanda aka fara gasar ligue ta ƙasar Niger da ake ma lakabi da SUPER LIGUE. A ƙarshen mako ne aka faro gasar Lik ta Jamhuriyar Nijar wacce ake wa laƙabi da Super Ligue.Ita dai wannan gasa ta Super League ta kasance kololuwar gasar kwallon ƙafa a ƙasar, inda ta ke ƙumshe da ƙungiyoyi 16, kuma babban birnin ƙasar Niamey ka dai na da club 12. A tsarin wasan kowa zai kara da kowa a gida da waje kamar yanda ake yi a sauran ƙasashe ke nan kowace ƙungiya za ta yi wasa 30. Haka kuma kamar a sauran ƙasashe zakaran da ta lashe wannan gasar za ta wakilci ƙasar a gasar ligue a matakin nahiyar Afrika da hukumar Caf ke shirya, don haka ɗaukacin waɗannan club ɗin ke maida hankali don ganin sun taka rawar gani a gasar. Kafin mu tsunduma cikin shirin bari muyi ratse don yin ɗaurayar yadda gasar ta gudana a bara tare da Magaji Minista mai sharhi ne kan harakar wasannin kwallon kafa.