Lafiya Jari Ce

Cutar Hanta ta Hepatitis nau'in B na yaɗuwa kamar wutar daji a Najeriya

Informações:

Sinopsis

Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan ciwon hanta nau’in B ko kuma Hepatitis B a turanci, cutar da masana ke gargaɗi game da yadda ta ke yaɗuwa kamar wutar daji tsakanin jama’a. Wasu alƙaluma sun nuna yadda ake da mutum fiye da miliyan 257 da ke fama da wannan cutar, a wani yanayi da Najeriya ke sahun ƙasashe 5 masu ɗauke da kashi 60 na masu wannan cuta a duniya baki ɗaya. Masana a ɓangaren lafiyar Najeriya sun bayyana yadda wannan cuta ta Hepatitis B ke yaɗuwa kamar wutar daji a sassan ƙasar, kuma abin dubawar shi ne yadda mutane da yawa ke rayuwa da cutar yanzu haka ba tare da sanin suna ɗauke da ita ba, kan hakan kuma muka nemi ji daga masana irin Dr Misbahu Sahabi na Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya da ke garin Birnin Kudun jihar Jigawa, wanda ke cewa tun farko cutar na da rabe-rabe wato mai haɗari da kuma mai sassaucin illa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.