Wasanni

Sauye-sauyen da aka samu a sabuwar gasar zakarun nahiyar Turai

Informações:

Sinopsis

Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan sauye-sauyen da a Ka samu a gasar cin kofin zakarun turai.A makon da ya gabata ne dai hukumar kula wasannin kwallon kafar Turai UEFA ta gudanar da hadin yadda wasanin rukuni na gasar zakarun Turai karo na 70 zai gudana, ganin cewa a wannan karon an samu sauye-saye da dama a gasar. Kadan daga cikin sauye-sauyen da aka samu sun hada da kara yawan kungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa daga 32 zuwa 36.Har illa yau, a wannan sabon tsarin hukumar ta sauya tsarin rukuni da a baya ake amfani da shi, in da a yanzu tazo da tsarin da ke kama da na lik-lik, inda kungiyoyi za su buga wasanni takwas maimakon 6 a matakin farko Kuma dukkanin kungiyoyin zasu kasance a teburi daya, sannan kungiyoyi 8 da suka fi yawan maki ne zasu wuce mataki na 16, wadanda suka kare daga mataki na 9 zuwa na 24 zasu sake neman gurbin ci gaba da zama a gasar sai Kuma daga 25 zuwa na 36 zasu koma gida ma’ana an yi waje rod da su.