Sinopsis
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episodios
-
Yadda aka sake samun ɓullar cutar Polio a Najeriya
12/05/2025 Duración: 10minShirin Lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba na musamman game da dawowar cutar Polio a Najeriya, cutar da alamu ke nuna nasarar yaƙarta ke yiwa ƙasar kwan gaba kwan baya, lura da yadda a lokuta da dama ake sake ganin ɓullarta bayan nasarar kawar da ita, kodayake ƙwararru sun ce wadda ta ɓulla a wannan karon ba wadda aka saba gani ba ce kuma bata kai waɗanda suka gabace ta illa ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............
-
Annobar ƙyanda ta tilastawa mahukunta Nijar yin rigakafin ƙasa baki ɗaya
05/05/2025 Duración: 10minShirin Lafiya Jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan shaushawar ƙyandar da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka jagoranta sakamakon ɓullar cutar wadda a duk lokacin da aka ga bazuwarta ta ke yiwa ƙananan yara illa matuƙa. Dai dai lokacin da duniya ta gudanar bikin makon rigakafi a ƙarshen watan Mayun da ya gabata, a Jamhuriyyar Nijar annobar ƙyanda ce ke ci gaba da yaɗuwa tare da galabaitar da ɗimbin ƙananan yara, lamarin da ya tilasta mahukunta ɗaukar matakan yiwa jama’a rigakafin wannan cuta mai haɗari.Cutar ta Ƙyanda ko Ado ko kuma Dusa na matsayin babbar matsalar kiwon lafiya ta yadda a duk lokacin da ta ɓulla ta kan haddasa asarar ɗimbin rayuka, kodayake a yanzu tuni ma’aikatar lafiya ta jagoranci aikin rigakafin na ƙasa baki ɗaya da zai shafi dukkanin ƙananan yara tun daga watanni 6 da haihuwa har zuwa shekarun 5 da nufin murƙushe cutar.Tsawon mako guda aka shafe daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Mayu ana gudanar da rigakafin na ƙyanda a sassan Nijar wanda aka yiwa ƙananan y
-
Yadda cuɗanya wajen amfani da moɗa ko cokali ke taimakawa wajen yaɗa cutuka
28/04/2025 Duración: 09minShirin Lafiya Jari ce na wannan makon, ya mayar da hankali ne kan nau’ikan cutukan da ke bazuwa sakamakon cuɗanyar da jama’a ke yi wajen amfani da kayayyakin da bisa ƙa’ida yakamata kowanne mutum ya yi amfani da nasa shi kaɗai. Har yanzu ana samun waɗanda ke yin gamayya wajen amfani da moɗar-shan ruwa ko cokali ko kuma kwanon cin abinci dama sauran kayakin da basu cancanci amfanin gamayya ba, lura da yadda cikin sauƙi hakan ke iya yaɗa cutuka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........
-
Matakan da ya kamata a ɗauka yayin kai ɗaukin gaggawa a lokacin faruwar haɗari
21/04/2025 Duración: 10minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakan da ya kamata mutane su riƙa ɗauka gabanin kai ɗaukin gaggawa a lokacin afkuwar haɗari ko ibtila'i, waɗanda rashinsu a wasu lokutan ke kaiwa ga asarar rayuka ko kuma haddasa gagarumar illa ga mutanen da haɗarin ya rutsa da su. Shirin ya shawarci jama'a game da samun ilimin iya kai ɗaukin gaggawa don kaucewa haddasa matsala ba tare da sani ba ga mutanen da ake ƙoƙarin ceton rayuwarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.