Sinopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodios
-
Har yanzu akwai rashin tabbas game samar da ingantaccen tsaro yayin gasar Olymics mai zuwa
06/05/2024 Duración: 09minShirin duniyar wasanni na wannan mako ya dubi yadda ake tufka da warwarwa game da tsarin samar da cikakken tsaro yayin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh
-
Nazari kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana
22/04/2024 Duración: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana. A makon da ya gabata ne dai aka kammala wasannin zagayen, inda aka fafata a wasanni 4. Dortmund da aris Saint-Germain da Bayern Munich da Real Madrid ne suka kaiga wasan kusa da na karshe a gasar ta bana. A yanzu Bayern Munich zata fafata da Real Madrid ita kuwa Borussia Dortmund ta kara Paris Saint-Germain.Ku letsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......
-
Hasashen yadda za ta kaya a gasar Firimiyar Ingila
15/04/2024 Duración: 09minShirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi. Yar manuniyar dai tuni ta fada kan kungiyoyin ukun saman tebur, wato Manchester City, Arsenal da Liverpool, lura da yadda suke kan kan kan a yawan maki, abunda ke kara nunawa duniya yadda gasar ta Firimiya ta ke ci gaba da jan zarenta a fagen tamola.Ko da yake a halin yanzu Manchester City ce ta karbe ragamar teburin wannan gasa, bayan rashin nasarar da Arsenal da kuma Liverpool suka samu a nasu wasannin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamsi Saleh.
-
Shiri na musamman kan shirye-shiryen gasar Olympics kashi na 2
08/04/2024 Duración: 09minA wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar. Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sunyi nisa, domin dai rahotanni na nuna cewar an kammala tanadin kusan dukkanin inda za a gudanar da wadannan wasanni.Sai dai wani hanzari ba guda ba, duk da matakan da kasar ta Faransa ta dauka na tabbatar da tsaron ‘yan wasa da kuma na ‘yan kallo, bayanai na nuna cewar akwai alamun fuskantar barazanar tsaro a lokacin gasar.Wannan lamari dai ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai birnin Moscow wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 140.A lokacin wata zantawa da aka yi shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon da ya gabata, ya ce babu shakka, akwai yuwuwar Rasha za ta kai hari a lokacin gasar da ke tafe.Kai hari a lokacin gasar OlympicsKai hari a yayi gasar guj