Sinopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodios
-
Yadda basuka su ka yi wa ƙasar Ghana katutu a cikin shekara guda
07/08/2024 Duración: 09minA yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024.Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024. A cewar babban bankin na Ghana, bashin da ake bin ƙasar ya karu ne zuwa Cidi biliyan 658.6 a watan Fabrairun wannan shekarar, tsabanin Cidi biliyan 611.2 da yake a ƙarshen shekarar 2023.
-
Yadda Najeriya ke fuskantar tashin farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 30
24/07/2024 Duración: 10minA wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata. Shin ko hakan zai kawo sauƙi kan halin da ake ciki a ƙasar? Kuna iya latsa alamar sauti don jin amsar wannan tambaya tare da masana ta cikin shirin...
-
Gwamnatin Najeriya za ta yi odan abinci daga waje saboda tsadar rayuwa a ƙasar
17/07/2024 Duración: 10minShirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin gwamnatin Najeriya na sahale shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa da wake da alkama da masara ba tare da biyan ƙudin fito ba har tsawon watanni 5, domin rage tasirin tsaɗar kayan abinci da ƴan ƙasar ke fama da shi tun bayan ɗarewar shugaba Bola Ahmed Tinubu mulki a bara. A wani taron manema labarai da ya kira wannan Litinin, ministan noma da samar da abinci na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana sabon matakin, inda ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ƙudin fito da kuma haraji kan muhimman kayan abincin ne har na tsawon kwanaki 150, domin wadatuwar kayan a Najeriya.Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ƴan kasuwa masu bukatar shigo da kayan abinci, ita kanta gwamnatin tarayya za ta shigo da alkama da Masara kimanin tan dubu 250 kowanensu, domin bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.